Top Local Places

Mahangar Arewa

, Kano, Nigeria
Company

Description

ad

Wannan filii na jaridar Mahangar Arewa, wadda take fitar a labaranta a kowanne wata don samarwa yan arewa yanci tare da zakulo musu sahihan labaraidaga karkara. Ba an bude ta bane don batanci ko cin zarafin wani ba, a'a sai don kyakykyawan manufofin arewa

CONTACT

RECENT FACEBOOK POSTS

facebook.com

Daga Aisha Usman Faruk JAMA'A DON ALLAH WA YASAN MAKOMAR MAMA TARABA A YAU? UBANGIDANTA ATIKU DAI YA KAURA ZUWA PDP.

facebook.com

ZA A YI WA DAN MAJALISAR KARAMAR HUKUMAR TARAUNI KIRANYE. Daga Rabi'u Muhammad Abu Hidaya Al'ummar karamar hukumar Tarauni cikin jihar Kano sun shirya tsaf domin yi wa dan majalisa mai wakiltarsu a garin Abuja kiranye, wato Honourable Nasiru Baballe Ila, a tattaunawarmu da wasu daga ciki dattawa da matasan karamar hukumar sun ce babu wani abin a zo a gani da wakilin na su ya tsinana tun darewarsa wannan kujera tsawon shekaru shida(6) idan aka yi la'akari da takwarorinsa na wasu kananan hukumomin jihar masu wakilci a Abuja kai har ma da kasa baki daya a cewarsu, don haka ba su ga dacewarsa a wannan kujera ba. kasancewa lokaci yana dada kurewa kuma ana ta samun abubuwan ci gaba a ko wacce karamar hukuma amma su a karamar hukumar Tarauni har yanzu shiru ake ji, a ci gaba da zantawarmu da wasu daga cikin al'ummar wannan yanki sun nuna cewa suna maraba da wannan kiranye da za a yi wa wakilin na su domin hakan kawai shi ne abin da zai sa sabon wakilin da za su aika ya yi musu aikin da ake bukata, da suke bayyana dalilansu na yin wannan kiranye sun ce " akwai ayyuka da kudirori da dama da yakamata a ce wakilin na su ya kai tun darewarsa wannan kujera, amma bai yi ba, hasalima akwai guraben aiki na ma'aikatun da suke karamar hukumar wanda yakamata a ce 'yan asalin karamar hukumar Taraunin ne suka samu aiki a ciki, a maimaikon haka ma sai wasu yan karamar hukumar ne suka samu tagomashin cin mariyar aiki a wadannan wurare, saboda halin ko in kulan da wakilan nasu yake da shi ga al'ummarsa, a maimaikon farilla sai ya buge da nafila wato a lokacin yin aiki da al'umma ke bukata sai ya buge da rabon babura ga wasu kalilin daga cikin mutanensa. Binciken mu ya gano yanzu haka mutane kimanin dubu shida sun sanya hannu a takarda da kwamitin kiranyen suka raba, mun kuma tattauna da wasu daidaiku a ciki jama'ar karamar hukumar wadanda suka sanya hannu a wannan takarda me yasa suke son dawo da wakilin na su ga abin da suka ce " Ya gaza game da hakkin da muka dora masa ya kuma sanya hijabi a tsakaninmu da shi, baya zuwa wurinmu tun lokacin da muka zabe shi ba mu kara sanya shi a idonunmu ba, ga shi kuma kullum matsaloli suna kara yi wa yankin namu yawa kwanakin baya mun mu da iyalanmu mun fama da zazzabin cizon saura da wasu cututtuka wadanda muke bukatar daukinsa na rabon magunguna, amma babu wanda yake saurara sai wasu mutane kalilan wadanda da ba sa tare damu". Lamarin yan siyasar kasar nan dai kullum sake tabarbarewa yake, hukumar zabe ta kasa ce dai ta bayyana wannan kudiri na kiranye a kwanakin baya don dawo da wakilan da su ka gaza ayyukansu a yayin wakilcinsu a majalisa kuma ga dukkan alamu lamarin zai samu tagomashi a cikin al'umma don bayan wannan dan majalisa na karamar hukumar Tarauni Honourable Nasiru Baballe Ila akwai wasu wakilan da ake yunkurin yi musu wannan kiranye. Za mu ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a wannan karamar hukuma don jin yadda za ta kaya tsakanin wannan wakili da al'ummar yankinsa.

facebook.com

facebook.com

facebook.com

facebook.com

facebook.com

facebook.com

facebook.com

http://www.hotpen.net/article-mahanga/2017/dalilin-da-ya-sa-na-ajiye-mukami-na-isa-pilot-0

facebook.com

http://www.hotpen.net/article-mahanga/2017/yadda-alumma-ke-fama-da-matsalar-tabarbarewar-tattalin-arziki-jihar-jigawa

facebook.com

Ciyarwa a watan Azumi yana da matukar muhimmanci Yan Uwa Mu hadu don Gudanar da ayyukan Alkhairi a cikin Watan Ramadan

facebook.com

facebook.com

Quiz

NEAR Mahangar Arewa