Top Local Places

Hausa A Arewa

Goron Dutse Aminu kano way, Kano, Nigeria
Media/news/publishing

Description

ad

Fadakarwa, nishadantarwa har ma da ilimantarwa, labarai da dumi-dumin su cikin harshen hausa sai ku lalubo  shafin [1:[0:1:HAUSA A AREWA]]

RECENT FACEBOOK POSTS

facebook.com

Tina baya shine roko allah yajikan takawa

facebook.com

ALLAH MUNA KARA GODIYA GAREKA KAMAR YADDA AKA SABA YAUMA MAL YA FARA DA DAGA AYATA 172 ZUWA TA 176 CIKIN SURATUL NISA'I WATO ZUWA KARSHAN SURA SANNAN MAL YA FARA KARANTO MANA AYA 2 DAGA CIKIN SURATUL MA'IDA ALLAH YA BAMU IKON YIN AIKI DA ABIN DA MUKAJI AMEEN

facebook.com

Via ZAUREN FIQHU Ranar da duk halitta zata taru.. Har Annabawa da Manzanni (as) kowa ta kansa yakeyi. Amma Annabinmu Muhammadu (saww) shi kadai ne yake ta al'ummarsa. Ranar da Allah yayi fushin da bai ta'ba yin irinsa ba, Kuma ba zai Qara yin irinsa ba, don haka dukkan Annabawa da Mala'iku babu wanda ya isa yin magana da Ubangiji ballantana ya nemawa kansa cheto ko al'ummarsa. Amma Annabi Muhammadu (saww) shi kadai ne darajarsa ta kai yayi magana da Rabbul Izzati Wal Jalali. Ranar da Jahannama zata zo tayi gunji tayi kururwa tayi ma kanta kirari, duk wanda ke cikin wannan filin na Alqiyamah kowa sai ya durkushe Qasa akan gwiwarsa saboda tsananin tsoro, in banda Annabi Muhammadu (saww). Ya Rasulallahi kai zaka je kayi Sujjadah ga Rabbul Malakuti, kayi masa yabo da kirarin da babu wata halittar da ta ta'ba yi masa.... Zai ce "YA MUHAMMADU YA MASOYINA! 'DAGO KANKA.. ROKI (DUK ABINDA KAKE SO) ZA'A BAKA.. KUMA KA NEMI CHETO A BAKA!! Babu wanda ya kai wannan Matsayin sai dai Kai.. Assalamu alaika Ayyuhan Nabiyyu wa Rahmatullahi wa barakatuhu. Assalamu alaika Ayyuhash Shafi'ul Mushaffa'. Assalamu alaika Ya Sahibal Maqamil Mahmud. Ya Allah ka taimakemu bisa Soyayyarsa da bin Sunnarsa da gaskiya, Ka kiyayemu daga sa'ba masa. Ka gafarta mana dukkan Zunubanmu, Ka kankare mana dukkan Kusakuranmu, Ka sanyamu cikin bayinka Salihai don falalarka da rahamarka. Ameen @hausaaarewa

facebook.com

HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD (S.W.A) WADDA YA YI A HUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARAFAT KENAN) ANNABI (SAW) YA FARA DA CEWA: “Ya ku mutane ku ba ni hankalinku, domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda ba su a wannan wuri a yau. Ya ku mutane kamar yadda ku ka riki wannan wata, (na Hajji) da wannan rana (ta Arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki ran Musulmi da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa mutane kayan da suka ba ku amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku. Ku tuna fa, hakika Allah zai yi sakayya akan ayukakanku. Allah (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi. Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana. Ya ku jama'a hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma su ma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akan ku da kuciyar da su, Kuma ku tufatar da su akan jin kai. ku bi da su kyakkyawan biyarwa. Ku kuma tausasa musu domin su majibintan al'amurran ku ne, kuma mataimakan ku, Hakki ne akan su da kar su yi abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci zina. Ya ku jama'a, ku yi kyakkyawar bauta ga Allah(SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, Ku azumci watan Ramadan, kuma ku bada zakka. Ku aikata aikin Hajji idan har kun samu damar yi. Ku sani fa, kowane musulmi dan'uwan musulmi ne. Dukkan ku daidai ku ke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai wajen tsoron Allah da aikata kyawawan ayyukka. Ku tuna fa (ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban Ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau. Ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka ku yi tunani sosai akan wannan magana da na gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai). Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); (Alkur ani) ga kuma (Sunnah). Idan kun bi wannan ba za ku taba bata ba. Duk wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, su ma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe su fi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada. Ya Allah ka zamo shaida a gare ni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.” 'Yan uwa ku yada wannan HUDUBAR ga 'yan uwa musulmi wadda kamar yau aka yi ta!!!

facebook.com

(KADA MU TOZARTA 'YA'YANMU MATA) "DAGA TASKAR BABAN MARYAM" DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI FADAKARWARMU TA YAU TALATA 6/RABI'UL AWWAL 1438 Zatayi Magana Akan:- MATSAYIN 'YA'YA MATA 'YA'YA Wata Amanace Da Allah SWT Yake Damkawa A Hannun Iyaye Domin A Jarabtasu Aga Yadda Zasu Kula Dasu Daga Cikin Iyaye kamar Yadda Yazoo Acikin Wasu Ayoyi Biyu Name Suratu SHURA Allah yana Baiwa Wasu 'Ya'ya Mata Wasu kuma Abasu 'ya'ya Maza wasu Kuma A Hadamusu Maza Da Mata wasu Kumar Sai a Kyalesu Hakanan Ba'a Basu Haifuwarba Duk yadda tafaru Ga Mutum Anyimasane Domin A Jarabashi Amma Kuma wasu idan Aka Basu Yaya Mata Sai surika Tozartasu Akan Hakane Manzo S,A,W Ya Bayyanamana Falalar Samun 'Ya'Ya Mata Dakuma Hani Daga Tozartasu kamar yadda yazo cikin wani Hadisi kamar Haka:- An Karbo Hadisi Daga Ibni Abbass Allah yakara Yarda Dashi yace:- Manzon Allah S,A,W Yace:- Duk Wanda Yakeda 'Diya Macce Bai Turbudetaba Kuma Walakantataba Bai Zabi 'Dansa Namijiba Akantaba Allah Zai shigardashi ALJANNAH Abu Dawuda Ya Ruwaitoshi Idan mukayi Nazarin Wannan Hadisi Zamuga Cewa Samun 'ya'ya Mata Yanada Matukar Falala Musamman Idan Mutum Yakula Da Hakki Dakuma Kulawa Tarbiyya Anan zan Kalubalanci Masu Fushi idan sun Sun Sami 'Diya Mata Su Sani Wasu Nacan Suna Neman Ko Wadanne Irine amma Basu samuba ALLAH KABAMU 'YA'YA MASU ALBARKA KO DAGA WANE JINSI SUKA FITO KUMA KABAMU IKON BASU TARBIYYA TAGARI AMEEEEEEEEEEEEEEEEEE­ EEEEEEEEN @ALH NAMADINA BABAN MARYAM Yana Yimuna Fatan Mun Tashi Lafiya @@@@@@@@@@@@@@@@@@@

facebook.com

(SHIN KO KASAN?? MATSAYIN DUNIYA A WAJEN ALLAH SWT) "DAGA TASKAR BABAN MARYAM" ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI FADAKARWARMU TA YAU TALATA 22/SAFAR 1438 zatayi Magana Akan:- "MATSAYIN DUNIYA A WAJEN ALLAH SWT" Shin ko kasan Matsayin Duniya A wajen ALLAH SWT? Karanta wannan Hadisi-: ﻋﻦ ﺳﻬﻞ ﺑﻦ ﺳﻌﺪ ﺍﻟﺴﺎﻋﺪﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﻟﻮ ﻛﺎﻧﺖ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺗﻌﺪﻝ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺟﻨﺎﺡ ﺑﻌﻮﺿﺔ ﻣﺎﺳﻘﻲ ﻛﺎﻓﺮﺍ ﻣﻨﻬﺎ ﺷﺮﺑﺔ ﻣﺎﺀ . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ FASSARA Ankarbo Hadisi Daga sahl bin sa'ad sa'idi Rta yace: MANZON ALLAH SAW yace: Matsayin duniya a wajen ALLAH Da yakai kai Daidai Da fiffiken sabro Da kafiri Bai sami koda kurbi Guda Na Ruwaba Acikintaba, Tirmizi ya Ruwaitoshi idan Muka Duba wannan Hadisi zamuga cewa yana koyardamu Duniya Ba Bakin komai Bace Akwai Ayoyin kur'ani Da Hadissai Dadama Da sukazo suna magana Akan Muguji Duniya SABODA HAKA YA ZAMA WAJIBI GAREMU MUDAUKI DUNIYA AMATSAYIN WANI FAGENE NA GYARAN LAHIRARMU ALLAH YABAMU IKON GUJEWA DUNIYA YA BAMU IKON KYAUTATA AYUKKANMU DOMIN GYARAN LAHIRARMU ALLAHUMMA AMEEEEEEEEEEEEEEEEN @ALH NAMADINA BABAN MARYAM yana yimuku fatan An Tashi Lafiya@ @@@@@ﺻﺒﺎﺡ ﺍﻟﺨﻴﺮ@@@@@@ @@@@@@@@@@@@@@@@

facebook.com

Hon. Dr. Abdulmumin Jibrin KOFA HAR YANZU RASHAWA DA CIN HANCI KARA KAMARI YAKE A ZAURAN MAJALISAR WAKILAI KARKASHIN MULKIN KAKAKIN NA MAJALISA DOGARA "Ba za a samu canji mai ma'ana ba sai da zage dantse mai wuyar ganewa, ni ina fatan zama cikin masu wannan hobasa" - Thomas Sankara Yau kwana na 88 da yunkurin KAKKABE DOGARA DAGA KUJERAR MULKI: A lokacin mawuyacin halin da tattalin arzikin kasa yake a ciki, amma 'Yan Majalisu da Ministoci suna awan gaba da makudan kudade da sunan hayar gidaje na shekara. Kakakin Majalisa Dogara da Lasun sun karbi Miliyan N500 na hayar gidajen daga hanyoyi biyu da sunan wai basu da Gidajen zama na Hukuma da Gidajen Shakatawa. Daga cikin ire-iren wannan tsare- tsare ne na rashin gaskiya babban maha'inci Herma Hembe ya dibi 'yan kallo da Lasun saboda wawure wasu cikin kudaden da shi Hon Herma yayi cikin kudaden na su. Ana sace biliyoyin Nairori da wulakantar da dukiyar kasa a shekara da sunan samawa 'Yan Majalisu gidajen kwana da wuraren shakatawa inda a karshe yake zama wuraren holewa da tara karuwai da sunan muhimman wuraren Gwamnati. Allah ya kiyaye! HON ABDULMUMIN JIBRIN PhD MBA APC-Kano Kiru-Bebeji Kano

facebook.com

SALAM FATAN AL KAIRI AGAREKU INA FATAN KUNA CIKIN KOSHIN LAFIYA AM MUNA BUKATAR MUJI SHAWARA DAGA GAREKU SABODA MUNA BUKATAR MU CHANJAWA WANNAN SHAFI SUNA ZUWA MUHADA KAI 'YAN AREWA

facebook.com

*RAYUWAR KILAKI KO KARUWA JAKAR MAZINATA ABIN TAUSAYAWA* . Via: Datti Assalafiy . A duk lokacin da naga yarinya ko mata mai zaman kanta wacce take sana'ar karuwanci nakanji matukar tausayinta, rayuwarsu abin tausayi ne, jin dadin karuwa na takaitaccen lokaci ne idan aka kwatanta da lokacin da ta dauko tsufa a harkan karuwanci. Duk wata shahararriyar karuwa da take tashe a harkan karuwanci takan dawo ta zama jangwangwan abin tausayawa bayan mazinata sun gama kacaccalata, bawai karuwa tana gadara da kyan jikinta ba, bari kagani ta dauko shekarun tsufa sai ka tausaya mata matuka Ita mazinaciya ko bata bayyana ba, siffarta bata boyuwa a wajen gogaggun masana harkokin yau da kullun, kana ganin mazinaciya zaka ganeta, ni tunda nake bincike akan wannan lamari ban taba ganin wata karuwa da ta doshi shekarun tsufa ba face sai na ganta da wata jinya na musamman a fatar jikinta. Rayuwar karuwa abin tausayine, idan karuwa ta tsufa har ciwon ajali ya kamata zakaga mai gidan da take zaune a wajenshi yana kokarin ya koreta daga gidan domin shi damuwarsa shine kada ta mutu masa a gida yasha wahalan kashe kudin da zai biya a fita da gawarta aje a bunne a daji Akwai wata shahararriyar karuwa musulma da mutu a hannun wani sai da aka rasa wanda zai mata sallah janaza har sai da ta kwana ta wuni, ko wanka ba'ayi mataba haka akaje aka bunneta bayan da jami'an tsaro suka shiga cikin lamarin. Wata karuwa bata jima da shiga sana'ar ba, bayan ta samu cikin shege sai rikici akan saurayi ya hadata da abokiyar sana'arta na karuwanci sai wanda rikicin ya hadasu ta dauki wuka ta cakawa karuwa mai cikin, wukan ya shiga ya kashe abinda ke cikinta, bayan kwana biyu itama ta mutu saboda ba'a samu damar kaita asibiti akan kari ba, har yanzu da nake wannan rabutu karuwan da tayi kisan tana state cid na Gombe kuma itama jinya ya gama cinye jikinta. Ya kai 'dan uwa matashi musulmi mai kishin addini shin kana cikin kungiyoyin matasa da sukan kai ziyara gidan karuwai domin ayi musu nasiha tare da maidasu gaban iyayensu? Ya kai 'dan uwa matashi ko kana da masaniyar cewa mafi akasarin 'yan mata da suke tserewa subar gaban iyayensu zuwa karuwanci ba'a son ransu bane wadanda da zaran sun samu orientation mai kyau zasu tuba su koma gaban iyayensu, shin kasan da haka? Anan ina amfani da wannan damar wajen mika sakon godiya da karfafa gwiwa ga wasu matasa musulmai masu kishin addini a garin Gombe wanda nake burin kowani musulmi yayi koyi dasu saboda abinda suke gudanarwa na alkhairi. A Gombe akwai wasu matasa da suka kafa kungiyar karkashin jibiyar wata kungiya ta musulunci, matasan sai ya kasance sun sadaukar da wani 6angare na lokacinsu, suka sadaukar da wani abu na dukiyarsu da suke samu wajen yin amfani dashi akan 'yan mata da suke barin iyayensu su taho sana'ar karuwanci, wadannan matasa sun sami nasara wajen maida adadi mai yawa na 'yan mata da suka fito sana'ar karuwanci gaban iyayensu, sannan idan dare yayi matasan sukan karkasu a manyan gidan karuwai na Gombe musamman sabon-layi suje su tsaya a kofar gidan karuwai, da zaran sunga matashi wanda bai kai shekaru 20 ba a kalla, zai shiga yayi zina sai su hanashi, wani lokacin ma sai a kama yaron a kaishi har gaban iyayensa, hakan yasa wadanna mata masu albarka suka samu gagarumar nasara wajen hana matasa samari aikata laifin zina. A rayuwa anaso duk inda musulmi yake ya zama wayayye da binciken kan yanda al'amura suke gudana cikin zamantakewa, mu dinga zuwa hatta matattara na mutanen banza don ganin yanda lamura suke gudana domin samun hanyar da zamubi mu maganceta. Ba da jimawa ba na taba kaiwa ziyara yankin da karuwai da mashaya suke anan garinmu Bauchi inda na tarar da wani kirista pastor irin masu bishara da daddare, yana rike da lasifika a hannunshi yana ta zabga wa'azi da nasiha irin nasu na kiristoci ga dandazon karuwai da mazinata da mashaya, anya mu musulmai bai kamata ace mune sahun gaba ba wajen gabatar da nasihohi a irin wannan a farfajiya na mutanen banza ba kuwa? Kada mu rena kanmu duk matsayin da Allah Ya ajiyemu mu sani yana da muhimmanci cikin addininmu na musulunci, kowa yana da damar ya bada nashi taimako da gudunmuwa ta hanyar da ya dace wajen magance manyan matsaloli irin wannan dake faruwa a cikin al'ummar mu. Muna rokon Allah Ya tsare mana imaninmu, Allah (T) Ya shiryar da karuwai da sauran mazinata su tuba su dena

facebook.com

Assalamu Alaikum yan uwa maza da mata kuci gaba da kasancewa tare damu kuma in allah zamu fara kokarin kawo muku shirye shiryan dazasu kawo mana cigaba arayuwarmu mu ' yan arewa tare dani #ABBA MUSA AYAGI

facebook.com

muna godiya da yadda kuke nuna kauna ga wannan shafi

facebook.com

Mamaki baya bari na kullum. Ban sani ba ko kuma kuna irin yadda nake tunani da mamaki. Ka je ka siyo Abu N100 jiya. amma ka koma yau ya zama 200. Wai me yasa? Me haka yake nufi? Ina mafita?

facebook.com

Quiz

NEAR Hausa A Arewa