Gangare Youths Forum - G.Y.F
Description
Wannan shafi mallakar Qungiyar Matasan Gangare ce (G.Y.F). Manufar mu sune "tunatarwa, ilmantarwa, da ma fadakarwa".
Tell your friends
RECENT FACEBOOK POSTS
facebook.comSPECIAL INVITATION. GANGARE YOUNG STUDENTS' ASSOCIATION (GYSA) cordially invites the General Public to her Annual End of The Year Congress and Public Lecture Tagged: Gangare Youths: A Symbol of National Transformation under the Distinguished Chairmanship of Alh. Sani Mu'azu, CEO LENSCOPE MEDIA,JOS. Guest Speaker: Alh. Ali Baba, Federal Road safety Commission. Special Guests of honour; Hon. Nazifi Ahmed, Honorable Commissioner For Information, Plateau State. Hon. Ezekiel Izang, Interim Chairman, Jos-North Local Government. Hon. Hassan Isa Mai Madara, Interim Secretary, Jos-North Local Government. Hon. Shehu Bala Usman, Jos-North's APC Local Government Flag bearer. Mrs Esther Ebanga, Chairlady WOWWI. Royal Fathers of the Day: Engr. Garba Hassan Turakin Dali. Alh (dr) Ibrahim Baninge, Chairman Baninge Herbal Medicine. Father of the day: Sheikh Sani Aliyu, Chief Imam Gangare Jos. Host: Mall Umar Aliyu, District Head. Date: Saturday, 23rd December, 2017. Venue: University of Jos Multipurpose Hall,Township Campus (old campus) Gangare,Jos. Time; 9:00 prompt. Note: This post should serve as invitation to those who we couldn't reach please. MAKE A DATE WITH US.
THE CAPACITY OF A WHEEL CHAIR-MAN: Abdullahi Ismail' also known as Abdullahi Rocky Boy is a Jos based business man who got crippled by automobile accident. His popularity as a regular radio caller is unprecedented in Plateau state and environs. He shot to fame after his marriage and the unfortunate accident between 2002 and 2015. Understanding the power of the wheel chair, Rocky boy persistently use his time to preach peace in the neighborhood of Gangare and Jos north local government thereby contributing towards cementing a bond of unity among Hausa, Berom, Anaguta, Rukuba and many other ethnic nationalities in the state. Boboye, the winning couch of the Plateau United once described Rocky boy as "an inspiration to the Plateau United players". His love for peace and egalitarianism has attracted several awards to him including the: (1)anti drug merit award; (2) ambassador of peace award; (3) transafrican links award; (4) the lookout fans award etc. Indeed, Abdullahi is the perfect description of a literary work of irony as he has demonstrated capacity in incapacitation". #see the value in you Credit: cmrd luka pampe
Gangare: Uwa Maba da Maman Alheri A daidai lokacin da shekarar 2017 ke mana sallama, tsakinin sati biyu an samu daman k’addamar da katafaren masallatai buyi a unguwar Gangare dake karamar hukumar Jos ta arewa a Jihar Plateau wanda kusan dukkanin mazauna unguwar Musulmai ne. Masallaci na farko, “AL – FURQAN”, an k’addamar dashi ranar litinin, 27:11:2017. Sannan an damk’a shi ga hannun Mallam Abu Muhammad domin ya kasance limami mai gudanar da khamsu salawat (salloli biyar na kowacce rana). Masallaci na biyu kuwa, wanda aka fi sani da “Massalacin (Alhaji) Saleh Hassan”, Massalacin Jumu'ah ne kuma an k’addamar dashi ne ranar Jumu'ah, 08:12:2017. An kuma maida shi wajan babban limamin Gangare, Mallam Muhammad Sani Baba yaro, wanda daman can shine limnamin Masallacin tun lokacin da aka samar da shi a shekarun baya don sauk’ak’ewa jama’ar Gangare da makwabta sakomakon rikice-rikicen da ya kai kusan shekaru 10 a baya wanda a kusan koyaushe ke haifar da sanya dokokin rashin ficewa nesa. Dukkanin Masallatan biyu, Architect Ibrahim Saeed ne ya zana su kuma ya kula wajan ginasu. Arc. Saeed haifanfen Gangare ne kuma nan ya girma yayi karatu har matakin degree a fannin zane. Wannan abun farinciki bai zo min da mamaki ba kasancewar na san Gangare da zama kan gaba a kullum idan ana maganan lamarin cigaban al’umma a garin Jos da kewaye ne. Da fari dai, ina mai al’faharin fa’din cewa, babu wata gwamnati ko kungiya, ta addini ko akasin haka a gida Nigeria ko waje da ke da alhakin gina wa’dannan katafaren masallatai guda biyu. Mutum ‘daya ne tal ya bigi kirji kuma ya samu tallafin Ubangiji wajan gina Masallacin farko na khamsu salawat, Alhaji Dr. Gambo Hamza. Masallacin Jumu’a kuwa, ‘daukacin Jama’ar wannan unguwace masu tarin albarka, mata da maza, manya da yara, masu halinmu da talakawa muka ha’da taro da sisi wajan gina shi. Muna fatan Allah Ya gina mana gidajen zama a aljannar Sa kamar yadda Yayi wa dukkan wanda ya gina masallaci dominShi alk’awari. Ka’dan cikin abubuwan alheri da unguwar Gangare ta zama kan gaba wajan aiwatarwa cikin ikon Allah sune: 1. Samar da k’ungiya mai zaman kanta ta Matasa a matakin unguwa wanda ko Gwamnatin tarayya ta amince da kafata k'ark'ashin jagorancin Alhaji Dr. Abu Tahir. Tun bayan kafa wannan k’ungiya mai suna Gangare Youth Forum (GYF) sama da shekaru goma da suka shu’de, wacce ta k’unshi duk wani mai fa’da aji a Gangare a matsayin majibinta (patrons), ta kasance matattaran alheri ne ga wannan unguwa. A yau, k'ungiyar na k'ark'ashin kulawar Mallam Adam Hamza shugaban Fityanul Isalam na jihar Plateau. 2. K’ark’ashin wancan k’ungiya ta Matasa ne Gangare ta zama farko wajan sayan motar agaji Fisabilillahi don kai gawa mak’abarata. Kuma ‘daukacin jama’ar Gangare ne dai sukayi karo – karo don sayan wannan mota wacce har yau tana nan k’ark’ashin kulawar GYF da taimakon jama’ar Gangare. 3. A wannan unguwa dai aka kuma fara samun wasu yaran matasa masu matukar kwazo da fatan alheri suka ha’da kansu waje guda suka kira kansu Gangare Young Students Association (GYSA) domin tallafawa yara marayu ganin suma ba a barsu a baya ba wajan karatu. Wa’dannan matasa da a yau, ba mu ka’dai ba, hatta gwamnatin jahar Plateau na alfari dasu na k’ark’ashin jagorancin Hafiz Abdussalam Aliyu Dawaki ne wanda bai jima da kamala karatun digirinsa na farko ba. Cikin ikon Allah kuma sun tallafawa yara marayu sama da 50 wanda wasunsu suna Jami’a a yanzu. 4. Biyo bayan tashe – tashen hankula da kuma rashin tsaro wasu unguwanin garin Jos suka samu kansu don kasawa daga wajan gwamnati, Gangare ce unguwa ta farko da tayi tunani kuma ta samar da ‘yan sintiri da a yau aka fi sani da “Vigilante” ko “Neighborhood” domin samar da tsaro a unguwar. A yau wannan abin alheri ya zama hantsi cikin garin Jos. Kowacce unguwa na da tata ‘yan sintirin kuma hatta gwamnatin tarayya tayi amanna da wannan yink’uri. 5. Banda irin wa’dannan abubuwan yiwa kai da unuguwannan ta zamto kan gaba, Gangarre na da tarihin samar da jin k’ai. A tsakanin 2001 – 2018 da aka dinga samun tashe – tashen hankula a Jos da kewaye, Gangare ce ta zamto ‘”tudun mun tsira” da kuma mafaka wa al’umma da dama daga k’auyika da dama da ma wasu ungunnani na kusa kusa da ita. Tsawon lokacin da wa’daannan mutane (da akafi ambata da ‘yanngudun hijira) suka zauna a wannan uguwa, sun sami kulawa ta ‘yan uwantaka dai dai gwargwado. Wasunsu ma nan suke zaune har yau, wasu sun yi aure daga unguwar sun kuma aurar. Shafi ‘daya ko buiyu ba zai iya daukan ‘dinbin tarin alheri da wannan unguwa ta Ganagare ta haifar ba a garin Jos da kewaye. A yau kowacce unguwa na kallo ne da kuma koyi da ita. Duk da cewa muna da matsalolin cikin gida kamar kowacce unguwa a garin Plateau, amma ba za mu ta’ba mantawa da tarin alheri da Allah Yai mana ba a wannan unguwa. Kuma har kullum a tsaye muke, kanmu da fatarmu, a matakin unguwa da kuma ‘dai-‘daikunmu, wajan ganin munyi maganin matsalolinmu. Zamu fahimci haka idan mukayi la’akari da cewa, a kullum mu matsalolin unguwar raguwa suke ba k’aruwa ba. Sa’banin sauran wurare. Kamar sauran shekaru da suka shu’de, wannan shekara ta 2017 zata gushe muna masu matuk’ar farin ciki kwarai. Muna fatan kuma a sabuwar shekara ta 2018, jama’ar wannan unguwa mai tarin albarka zata maida hankali wajan wani abin kuma mai matuk’ar muhimmanci kamar cigaba da gina masu sallaa tunda an samar musu da masallaci. Muna fatan matasannan namu zamu k’ara k’aimi wajan neman ilimi da kuma dogaro da neman na kanmu. Bayan addu’a ta dukkanin alheri ga ‘daukacin al’ummar Gangare, naza da mata, zan rufe wanna rubutu, a yau, da shawarwarin Mallam Abubakar Nasiru kamar haka: “Muna fatan limamanmu na wa’dannan sabbin masallatai da sauran masallatai zasu cigaba da amfani da damar da Allah Ya ara musu ta kiran mutane ga daidai da kuma ha’da kan al’ummar Gangare. Ina fatan Mallamai, Dattawa da Attajiran wannan unguwa zasu k’ara k’aimi wajan jan Matasa a jiki. Su fahimci cewa dukkaninsu Allah Ya bamu su ne matsayin alheri.” Ga dukkanin mai wata shawara ko tsokaci, na baku daman yin hakan a wannan shafi nawa. Kuma ina tabbatar muku da cewa shawararku zasu kai ga inda kuka nufa cikin ikon Allah. Misbahu Elhamza 12/9/2017
Today is exactly seven(7) days since you left this sinful earth. You left when we most needed your simplicity, generosity, hospitality and above all, your jovial character(worth emulation) towards everyone that comes across you. We will never forget the memorable life we lived with you. In fact, living with you is a school for us where we learned how to even live life itself. My prayer is always for Allah to grant you the highest rank of #Aljannah and highest position in the #Jannah. We #Love but Allah loves you most. #GoodBye #BabaKallah
It was a tremendous effort by the Gangare youth forum's security committee bringing all the aspirants contesting for councillorship in Gangare on board to iron out some security threats. All of the contestants agreed to go back and discuss widely with their supporters in order not to engage in any #Pre_election or #Post_election violence. Kudos to Nasiru Na'aga(committee chairman) for a swift action on this matter. Allah yabawa mairabo sa'a
Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un! Muna mika ta'aziyarmu ga iyalai da kuma daukacin Jama'ar wannan unguwa na rashin Mal. SHEHU ALKA, limamin Masallacin barandar dake jikin gidan Sale Hassan. Wato mahaifin (baba) Sale Dan Kurciya. Za ayi janaizarsa Mallam a yau, a Masallacin Jumu'ah na Sale Hassan, bayan sallar Jumu'ah In Sha Allahu. Allah Ya gafarta mishi. Ya kyautata makoma. Amin. - Gangare Youth Forum
Innalillahi wa inna'ilaihi raji'uan! Mun samu labarin rasuwar Alhaji Ahmadu Driver dake Sabon Layi. Alhaji Ahmadu daya ne cikin dattawanmu Na wannan unguwa mai tarin albarka. Muna fatan Allah Ya yiwa Alhaji Rahama. Ya kuma baiwa iyalai da abokanan arziki hakurin rashi. Amin.
Inna lilLahi wa inna'ilaihi raji'un! Mun samu labarin rasuwar Bakura, wanda akafi sani da suna "Bakura Police" a jiya da daddare sakamakon shock na wutar lantarki. Ana Jana'izar Bakura yau da safennan, a nan gidansu dake Layin Barebari. Muna fata Allah Ya gafarta wa Bakura. Allah Ya bamu da 'yan'uwansa hakurin juriya.
Serving the community.
"Gangare Community Denies Attacks on Igbo": https://www.dailytrust.com.ng/gangare-community-denies-attacks-on-igbo.html And now that Daily Trust had published our protest to the allegation on our community, Gangare, we hope it get to the person in question, the Director General of Plateau State Peace Building Agency, Mr. Lengman. It is our hope also, as stated elsewhere, that he will be verifying every information he received before going on air as misleading information can have far reaching consequences on any community.
Gangare Youth Forum: Our Stand On The Confusion That Trailed The IPOB Saga In Jos On The 14th September 2017 It is with great sense of responsibility that we wish to express our displeasure over the assertion of the Director General, Peace Building Agency in Plateau State, Mr. Joseph Lengmang in an interview with a VOA reporter Mrs. Zainab Babaji to the effect that Gangare Community was one of the scene of the skirmishes that trailed the IPOB saga in Nigeria's South East region. This assertion is, with all due respect not correct and misleading in its entirety. The Gangare Community is a law abiding community that can never allow its inhabitants to embark on such lawlessness. Every resident of Jos is aware of the places that such skirmishes took place and, surely, Gangare is not one of such places. We see such allegation against our community as a deliberate and fallible attempt at mischief in order to tarnish the image of our law abiding community. We hereby call on Mr Joseph Lengman, as a Peace Activist to verify every information he received before going on air as such misleading information can have far reaching consequences on a community working hard to ensure peaceful coexistence among the diverse residents of Jos. We at Gangare will continue to support the peace efforts of Governor Simon Bako Lalong to ensure that the peace we now enjoy in Plateau State is sustained. We call for continued vigilance on the part of the security agencies to ensure that those that took laws into their hands are fished out and dealt with accordingly. To this, we reiterate our unflinching support to the security agencies and the state government. May God continue to bless and keep our Plateau and the Federal Republic of Nigeria peaceful. SIGNED: Mr. Sama'ila Garba Secretary, Gangare Youth Forum September 17th, 2017.
The Gangare Youth Forum's Committee on "Health and Sanitation" today, September 12, 2017, took a surprised visit to the community's clinic. The visits was to access the 'service delivery' by the workers, and to also see where we as community will come in. We also went round the clinic and access its base on the facilities on ground. Ganagre First ... - Abubakar Nasiru For media and publicity