Top Local Places

Jibwis Bauchi State

Gwallaga central Masjid Murtala Muhammad way Bauchi, Bauchi state Nigeria, Bauchi, Nigeria
Church/religious organization

Description

ad

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

An kirkiri wannan shafi ne domin bada gudumowa wajen da`awaah ta Alqur`ani da Hadithi a bisa fahimtar magabata.

RECENT FACEBOOK POSTS

facebook.com

#SANARWA! #SANARWA!! #SANARWA!!! Kungiyar JAMA'ATU IZALATU BID'A WA IQAMATUS SUNNAH na jihar Bauchi, wanda #Alh. Muhammadu Inuwa Dan'asabe yake jagoranta, suna farin cikin Gayyatar Dukkan jama'a zuwa gagarumin #WA_AZIN_JIHA da ta shirya kamar haka;- #Rana:-Lahadi 22-10-2017CE #Lokaci:-Bayan Sallar la'asar #Wuri:-Karamar Hukumar Alkaleri #Malamai -Al-sheakh Sulaiman Yusuf Bashir -Mal. Manga Misau -Barr Garba Hassan -Dr. Ibrahim Adam Disina -Al-Sheakh Muhammad Kabir Azare -Mal Adamu Bello -Mal. Zakariyya Muhammad Fegin makafi -Imam Ahmad Usman -Mal. Hashimu Rabiu -Mal. Salisu Kwankiyal -Imam Abdulrahman Idris #Alarammomi:- -Alaramma Adam Adam -Alaramma Abubakar Usman -Alaramma Auwal Biyadihi -Alaramma Sabo Muhammad Miya ALLAH YABADA IKON HALARTA, AMEEN. #JIBWIS_SOCIAL_MEDIA #BAUCHI_STATE 20-10-2017CE

facebook.com

Khuduban Sallar Juma'a daga Masallacin Juma'a na Abu Huraira dake GRA Bauchi. Tare Ustaz Muhammad Sadisu Alhaji Sani (Na'ibi Na daya) kuma Shugaban Jibwis Bauchi zone. Maudu'i Suffofin Mutum Mummini. Malam ya lissafo siffofi daya yawa Wanda ya kamata a samu mutum Muslimi dasu musamman wajen riko da addini da iya zaman takewa da alumma da kuma kyautatawa iyali. Allah ya saka wa malam da alkairi.

facebook.com

KUNGIYAR JIBWIS TA JIHAR BAUCHI TA KAI ZIYARAR GAISUWAR TA'AZIYYA A JIHAR GOMBE A yau Talata 17/10/2017 Tawagar Jibwis ta Jihar Bauchi karkashin Jagorancin Shugabanta Alh. Muhammad Inuwa Dan'asabe takai ziyarar ta'aziyya wa iyalai da 'Yan uwan Shugaban Jibwis na karamar hukumar Gombe Mal. Dan Musa dakuma Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami wanda shima Allah yayi rasuwa wa Mahaifiyarsa duk a garin na Gombe. Tawagar ta fara da zuwa gidan Marigayi Dan Musa wanda shugaban Jibwis ta Jihar Gombe Engr. Muhammad Salisu Gombe shine ya tarbi tawagar tare da iyalai da yan uwan mamacin. Shugaban Jibwis ta Jihar Bauchi Alh. Muhammad Inuwa Dan'asabe shine ya fara jawabi tare da gabatar da Ta'aziyya game da wannan rashi, Shugaban Wanda ya nuna kaduwansa game da rasuwan wannan bawan Allah, yace wannan rashi ne na alumman kasa baki daya bawai iya na iyalai da 'Yan uwa bane kawai. Anashi jawabin shugaban Jibwis ta Jihar Gombe Engr. Muhammad Salisu Gombe yayi matukar godiya bisaga wannan Ta'aziyya, daga karshe yayi addu'ar alheri ma wannan tawagar mai karfi daga Jihar Bauchi. Tawagar ta zarce gidansu Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami yayinda ta samu 'yan uwa da 'yaya na marigayiyar ciki harda shi kanshi Dr. Ali Pantamin. Yayinda Shugaban tafiyar Alh Muh'd Inuwa Dan'asabe yayi jawabi a madadin Jibwis ta jihar Bauchi, Shima anashi jawabin Dr. Pantami yace irin wannan gaisuwa badai taba mantawa da kungiyar Izalah ta Jihar Bauchi ba, Daga karshe yayi addu'ar Alheri wa tawagar yakuma Aduu'an Allah ya saukesu lafiya. Kadan da cikin wanda suka samu Halartan wannan tafiya sun hada da: 1. Alh. Muhammad Inuwa Dan'asabe Chairman Jibwis Bauchi 2. Alh. Ahmad Yaya National Treasurer Jibwis Nigeria 3. Alh. Mutari Abdulkadir National Admin Secretary 4. Imam Ibrahim Idris Chief Imam Gwallaga Masjid 5. Alh. Muhammad Sabitu Yusuf Director F.A.G 6. Ustaz Muhammad Sadisu Alhaji Sani Chairman Jibwis Bauchi Zone 7. Malam Ahmad Ibrahim Deputy National Circler Bearer F.A.G 8. Malam Alhassan Suleiman Director Da'awa Jibwis Bauchi 9. Malam. Abdullahi Tambari State Intelligent Officer Da dai sauran alumma dama ciki harda social media da 'Yan Agaji. Muna aduu'an gafara wa mamatanmu, Ameen. JIBWIS SOCIAL MEDIA BAUCHI STATE 17/10/2017

facebook.com

Tawagar Jibwis ta Jihar Bauchi karkashin Jagorancin Shugaban ta Alh. Muhammad Inuwa Dan'asabe ta a kama hanyar tafiya garin Gombe domin gabatar da Ta'aziyyar rasuwan Shugaban Jibwis ta karamar Hukumar Gombe, da Mahaifiyar Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami, Wanda Allah ya karbi rayuwar su ranar Lahadi data gabata. Cikin tawagar akwai 1. Alh. Muhammad Inuwa Dan'asabe Shugaban Jibwis Bauchi 2. Imam Ibrahim Idris Chief Imam Gwallaga 3. Alh. Mutari National Admin Secretary 4. Alh. Ahmad Yaya National Treasurer 5. Alh. Muhammad Sabitu Yusuf Daraktan Agaji Na Jihar Bauchi 6. Ustaz Muhammad Sadisu Alhaji Sani Shugaban Jibwis Bauchi Zone 7. Alh Ahmad Ibrahim Deputy National circler Bearer Da dai sauran Jama'a da dama ciki harda Social Media da Yan Agaji Muna bukatar addu'ar ku.

facebook.com

AN GUDANAR DA YAYEN DALIBAI A MASJID USMAN BN FODIO RH G.R.A BAUCHI. A ranar Asabar 14-10-2017 an Gabatar da yayen Dalibai a makarantar Sheikh Usman Bn Fodio dake New G.R.A Bauchi, taron wanda akayi karkashin jagorancin Alh. Muhammad Yunusa Muhammad (Yariman Ningi). A cikin jawabinsa Sheikh Dr. Mansour Isah Yelwa ya gabatar da nasiha ne akan falalar Hada masallaci da Makaranta waje guda. Daga bisani ya ja hankalin akan Mahimmacin Taimakawa Addinin Musulunci. Manyan baki da suka samu halartan wannan yayen dalibai akwai. 1. Dr. Baba Muhammad Gidado (Madakin Bauchi) 2. Prof. Ladan Salihu 3. Alh. Dalladi Abubakar Sarkin Fadan Miri (Maza Wajen Bauchi) 4. Dr. Danjuma Adamu Dabo 5. Dr. Mansur Isah Yelwa 6. Dr. Umar Alka 7. Alh. Alhassan Suleiman (Ajiyan Dass) 8. Alh. Hassan Adamu Shira Da dai sauran ma halarta da dama. Daga Karshe Sheikh Shuaibu Hassan Shinge Shi ya rufe wannan Taro da Addu'a ya kuma yi fatar Alheri ga wannan Dalibai da Aka yaye su. Jibwis Social media Bauchi state Nigeria 25-01-1439AH 15-10-2017CE

facebook.com

*SANARWA SANARWA SANARWA* A madadin Dalibai da Kwamitin Masallacin Umar bn Khaddab (Masallacin Dr Zubairu Madaki) Muna Sanar da Al'ummar Musulmi da Daliban Ilimi, cewa Babban Malamin mu, *Sheikh Dr Zubairu Abubakar Madaki* Zai koma Dukkan Karatukan da yake Gabatarwa Yau Juma'a 13/10/2017, Insha Allah, kamar haka:-- *KARATUN DARE BAYAN MAGRIB* ********************************* 1.Ranan Juma'ah da Asabar • Littafin Mukhtasarus Siratur Rasul (na Muhammad bn Abdulwahhab). 2. Ranan Lahadi:- • Littafin Alfiqihul Muyassar. *KARATUN ASUBA* ******************* 3. Ranan Litinin da Talata:- • Littafin Askariy 4. Ranan Alhamis da Juma'ah:- •Littafin Riyadis Salihin. *5. KARATUN MAJALASI* ************************ Ranakun Litinin, Laraba da Alhamis, bayan Sallan Magriba. • Karatun Daliban Ilimi, na Majalasi. Allah ya bada ikon halarta, da Fahimtar karatun. *JIBWIS SOCIAL MEDIA* *BAUCHI L.G.A* 23/01/1439 AH 13/10/2017

facebook.com

A yammacin yau alhamis ne Babban Sakataren kungiyar Jibwis ta kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya ziyarci garin Bauchi domin duban wasu dattawa da suka Dade suna gwagwarmaya a Wannan Kungiya domin rashin lafiya da suke fama dashi. Sarkin Malaman Ajiyan Bauch Malam Hamza Muhammad da Alaramma Yahuza Muhammad Bauchi saka makon rashin lafiya da suke fama dashi. Shugaban Kungiyar Jibwis ta Jihar Bauchi Alh. Muhammad Inuwa Dan'asabe shine ya Jagorancin tawagar Wanda kunshi wasu mashahuren mutane, 1. Malam Muktar Admin National Admin Secretary 2. Alh. Ahmad Yaya National Treasurer 3. Ustaz Muhammad Sadisu Alhaji Sani Chairman Jibwis Bauchi Zone 4. Alh. Ahmad Ibrahim Deputy Circular Bearer F.A.G Daga karshe Sheikh Muhammad Kabiru Gombe ya samu damar zagayawa wasu daga cikin dakunan dake Asibitin Koyarwa na Jami'an Abubakar Tafawa Balewa Bauchi domin gabatar da gaishe gaishe ga sauran majiyyantan dake cikin asibitin. Muna addu'ar Allah ya basu lafiya mu kuma da muke da lafiya Allah kara inganta mana ita Ameen. Jibwis Social Media Bauchi State 12/10/2017

facebook.com

#SANARWA! #SANARWA!! #SANARWA!!! A madadin Makarantar #USMAN_BN_FODIO_COLLEGE_OF_ARABIC_AND_ISLAMIC_STUDIES dake New GRA Bauchi. Suna gayyatar Al'umma #Yayen_dalibansu_karo_na_Farko wanda zai gudana kamar haka: #DATE: #Asabar Muharram 23rd, 1439, (Oct 14, 2017) #LOKACI: Karfe Goma na safe 10:00am #VENUE: Harabar makarantar dake #New_GRA, kusa da Gidan Kaura, Bauchi. Allah yabada ikon halarta, Ameen #JIBWIS_SOCIAL_MEDIA #BAUCHI_STATE 11/10/2017

facebook.com

KUNGIYAR JIBWIS BAUCHI ZONE TA GABATAR DA BABBAN TARON MITIN TARE DA YAN MAJALISAR ZARTASWA. Jiya Lahadi ne kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa'Iqamatis Sunnah ta Shiyyar Bauchi, Karkashin Jagorancin Shugaban ta Ustaz Muhammad Sadisu Alhaji Sani, ta gudanar da Babban Taron Mitin a Masallacin Juma'a na Abu Huraira dake nan Garin Bauchi. A cikin Jawabin sa Shugaban Ustaz Muh'd Sadisu Alhaji Sani, Ya nuna matukar farin cikin sa dangane da ganin taron yasamu mahalarta daga dukkan Karamar hukuma dake shiyyar, Sa'annan Yakara dacewa taron an shirya shi ne don ciyar da kungiyar gaba, da samar da hayoyin dogaro da kai. Sa'anan yaja hankalin mahalartan kan yin aiki don Allah batare da tsoron masu zagiba. A karshe ya yabawa Gwamnan Jihar Bauchi Barr. Muhammad Abdullahi Abubakar bisa ga gudumawar dake bawa wannan Kungiya, daga nan Yayi Addu'an Allah yayi wa Gwamnan Jagoranci don sauke nauyin da Allah ya daura masa na Jagorantan al'umma. A nasa Jawabin Shugaban Kwamitin Social Media na Bauchi Zone Ustas Abdulmalik Aliyu Abubakar Ya yabawa Shugaban Jibwis Bauchi Zone bisa gudumawar dake bama Kwamitin don gudanar aiyukan su, Daga nan ya nemi shugaban da ya kara tallafa wa Kwamitin da kayan Aiki dasu kara taimaka ma Kwamitin wajen gudunar da ayyukansu cikin Nasara. Taron yasamu mahalarta daga kananan hukumomi kamar haka:- 1. Alkaleri 2. Bauchi 3. Bogoro 4. Dass 5. Darazo 6. Ganjuwa 7. Kirfi 8. Ningi 9. Toro 10. Warji 11. T/Balewa Taron ya amince da abubuwa kamar haka:- 1. Gudanar da Babban Taro Sau Hudu(4) a shekara 2. Gudanar Manyan Wa'azi sau Hudu(4) a shekara 3. Ziyarce Ziyarce sau Hudu(4) a shekara 4. Gudanar da Taron karawa Juna Sani (Seminar) Sau Daya (1) a shekara. 5. Nada Kwamitin Tattalin Arziki da Samarda hanyan dogaro da Kai, 'Yan Kwamitin sune:- 1. Malam Ahmad Sulaiman LK 2. Alh. Bashir Sa'ed Bogoro 3. Alh. Tasi'u Iliya Abdul'Azeez Darazo 6. Wa'azin Zone a Farkon Watan Nuwamba na Wannan Shekarar. Allah ya bada ikon aiki da abubuwan da aka tattauna yasa su zama hanyar cigaban Wannan Kungiya dama addini Musulinci gaba daya. JIBWIS SOCIAL MEDIA BAUCHI ZONE 19/01/1439 AH 09/10/2017

facebook.com

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN Amadadin Kwamitin Jibwis Social Media Bauchi Zone, daukacin Shuwagabannin da Mambobin Kwamitin. Muna mika sakon ta'aziyya ga Shugaban Jibwis Bauchi zone Ustaz Muhammad Sadisu Alhaji Sani (Na'ibin Masallacin Juma'a na Abu Huraira GRA Bauchi) bisaga rasuwan Mahaifin Matar sa, Alh. Sani Gwaram ta Kari. Wanda Allah ya karbi rayuwar sa ranar Juma'a data gabata bayan yayi fama da jinya ta dan wani lokaci. Muna addu'an Allah ya jikansa da rahama ya gafarta masa ya kyautata makoncin sa ya albarkaci zuriyar da ya bari Ameen. Jibwis Social Media Bauchi State 09/10/2017

facebook.com

#KARATUN_MATASAN_SUNNAH #LIVE_UPDATE #TA_ALIQI_NA_BIYU #Malam_Usman_Ibrahim_Gi_ade Yau Lahadi 08/10/207 committen matasan sunnah na Bauchi LGA suke gabatar da Karatu a Babban Masallacin Juma'a na Umar ibn khattab dake Kofar wambai anan cikin garin Bauchi. Allah yasa mu amfana da Abinda malam yake fada. #JIBWIS_SOCIAL_MEDIA #BAUCHI_STATE 08/10/2017

facebook.com

#KARATUN_MATASAN_SUNNAH #MALAMI_NA_BIYU #Imam_Ibrahim_Ahmad_Burema Yau Lahadi 08/10/207 committen matasan sunnah na Bauchi LGA suke gabatar da Karatu a Babban Masallacin Juma'a na Umar ibn khattab dake Kofar wambai anan cikin garin Bauchi. Allah yasa mu amfana da Abinda malam yake fada. #JIBWIS_SOCIAL_MEDIA #BAUCHI_STATE 08/10/2017

facebook.com

Quiz