Jibwis Rimi Social Media Katsina
Description
Wannan Page an budashi don tunatar da juna abunda ya shige masu duhu kuma baya nuna banbanci akida.
Tell your friends
RECENT FACEBOOK POSTS
facebook.comINNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN A yanzu da Misalin karfe 2:17 na daren Larabar nan nake samun Labarin rasuwar Babban Malami na Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Ikamatis Sunnah Rimi watau Malam Abubakar Umar Rimi, ya rasu bayan fama da doguwar Jiyya ta akalla Shekara da watanni. Ya rasu yabar 'Ya 'ya da Jikoki, daga cikin Yayanshi akwai: 1. Malam Bashir Abubakar Umar NUT Chairman Rimi, JIBWIS Social Media Chairman kuma Babban Malami na Kungiyar Izala. 2. Malam Abdullahi Abubakar (Hafizi) Shugaban Majalisar Malamai ta Izalar Rimi 3. Malam Aminu Abubakar (Lover)* Malamin Makaranta. Za'ayi Jana'izarshi a gobe Alhamis da Misalin karfe 8:00 na safe in Allah ya kaimu. Fatan Allah ya jikanshi ya kyautata namu karshen ya hadamu a Aljannarsa Madaukakiya. Jibwis Rimi ©1438/2017
إِنَا لِلَّهِ وَإِنَا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ A madadin kwamitin kafar sadarwa na Jibwis Rimi watau Jibwis Social Media Rimi muna mika Sakon ta'aziyarmu ga dukan Ahli na Marigayi Dr. Alhassan Sa'id Jos da kuma Shuwagabannin izala na kasa hakika wannan rashi ba karamin rashi bane ga kungiyar izala dama duniya baki daya kaucewar Malami irin wannan ba tare da samun wanda ya maye gurbinsa ba. Fatan Allah ya bada hakurin jure rashi ya sadamu dashi a Aljannar Firdausi Ameen. Jameel Ahmad Rimi Secretary JSM Rimi State EXCO ©1438
Jibwis Kaduna Babu ruwan Izala da rikicin Shi'ah da mutanen gari! Kawai abin da izala ta fadi shine Ta goyi bayan matakin da gwamnantin jihar Kaduna ta dauka akan ayyukan 'yan Shi'a. Amma rikicin shi'a da mutanen gari wannan bai shafi Izala ba. Haka zalika Izala Tana kiran mutane da su daina daukan irin wannan hukunci a hannunsu, wannan aikin jami'an tsaro ne, kuma aikata irin wannan ta'asa zai zama da zunubi tare da amsa tambaya ranar gobe kiyama. Da fatan za'a bi doka da oda a duk lokacin da irin hakan ya aso.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! A madadin kungiyar JAMAATU IZALATUL BID'AH WA IQAMATUS SUNNAH muna masu sanar daku lokacin fara sallar Idi da za'a gudanar kamar haka: 1. RIMI ¤MASSALACI: JIBWIS eid mosque @ GDSS Rimi ¤ LIMAN: Imam Lawal Yakub Rimi ¤LOKACI: Karfe 9:00 na safe *********************** 2. TSAGERO ¤ WURI: Tsagero Jibwis jumaat mosque bakin kasuwa. ¤LIMAN: Malam Abubakar Mai Kano ¤LOKACI: 9:00 ================= 3. ABUKUR WURI: Abukur eid mosque LIMAN: Abukur Juma'at Imam LOKACI: 9:00 Haka kuma wannen tsarin yake a sauran kowane masallatai. JAMEEL AHMAD RIMI STATE JSM EXCO SECRETARY JSM Rimi
DOMIN SAMUN TAFSIRIN MALAMAN SUNNAH Kasance da website ta sunnah a www.darulfikr.com domin dadadawarku da nishadi hadi da wa'azantarwa. Jameel Ahmad Rimi Secretary JSM Rimi
Assalamu alaikum
KHUDBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN KOFAR YAMMA RIMIN KAURA KT MAI GABATARWA-M.LAWAL YAKUBU RANA-3-5-1437=11-02-2016 LOKACI1:30-2:00PM TAKE-ZUCIYA DA AIYUKAN TA. A khutbar sa ta farko bayan Yabo ga Allah madaukakin Sarki da salati ga Annabi(saw)ya karanto ayoyi uku na khutbatul hajah sannan yaci gaba da bayani a inda ya kawo wata qissa wadda sahabin Manzon Allah(Abdullahi Dan Abbas ya kawo) ta wani bawan Allah dan -aljannah,Wanda Annabi (saw)wata rana yake cewa sahabbai(RA)ga Dan -Aljannah nan tafe sai akaga wannan bawan Allah ya iso.Kuma anyita haka kamar sau uku. Sai Abdullah Dan Abbas yace shi kuwa sai yaga mi wannan Sababin yake yi har ya samu wannan tabbaci.Sai ya bishi gida a matsayin Bako har tsawon wani lokaci Amma sai yaga da yayi Shafa'i da Wuturi sai ya kwanta. Daga karshe dai Sahabi Abdullahi Dan Abbas ya tambaye shi yace mashi naji Annabi(saw)ya ambace shi a cikin 'yan- Aljannah.Kuma baiga wani gagarumin aiki da yake ba.Sai wannan sahabi ya gaya masa cewa bai taba yiwa wani hassada ko kuma ya qullaci wani a ransa ba tunda yake. A hudubarsa ta biyu ya karanto wasu ayoyi da hadisau masu nuni akan haka. Daga karshe ya rufe Khutbar sa ta yiwa dukkanin Musulmi addu'a da fatan Allah ya daukaka Musulunci ya kaskantar da kafurci. Bashir Abubakar Umar Chairman JSM Rimi Local Gov't 3-Jumada Ula-1437= 11-02-2016.
KHUDBAR JUMU'A DAGA MASALLACIN K/YAMMA RIMIN KAURA GABATARWA:MAL.LAWAL YAKUBU LOKACI:1:30-2:00PM TAKE:MUHIMMANCIN SANA'A DA KASUWANCI 12-04-1437 22-01-2016 Bayan yabo ga Allah da Salati ga Annabi(saw)Mal yayi bayani akan muhimmanci Sana'a ya karanto ayoyi da hadisai da suka yi magana akan haka,kamar Qissar Zulqarnain da sauran su. Ya cigaba da cewa bisa wadannan dalilai"ya zama dole ga Mahukunta dasu Samar da sana'o'i ga Al'ummar su.Bai dace ga Al'umma musulma ba data san wannan ta zauna babu masana'anta." A khudbar sa ta biyu ya nuna muhimmacin kasuwanci,ya karanto ayoyi a cikin Al-qurani da hadisai da suke magana akan haka.yayi kira ga Musulmi dasu riqi kasuwanci. A kasuwancin yayi magana akan kiyaye fadama Riba(usury) da Kuma ha'inci watau(Algushu).Yayi magana akan cewa kowane mutum yana da bukata da bayuwa ga dan-uwansa shi yasa Allah ya bore mana kusuwanci domin mu taimaki juna . Daga karshe yayi addu'a Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi baki daya,kuma Allah ya qasqantar da Kafurci da Kafurai. Bashir Abubakar Umar, Chairman JIBWIS Social Media Rimi, 12-Rabi'u Akhir 1437, 22-01-2016
HUDUBAR JUMU'AH DAGA MASALLACIN JUMU'AH NA K/YAMMA GARIN RIMI MAI GABATARWA :M.LAWAL YAKUBU RIMI LOKACI:1:30-2:00pm 5 Rabi'ul Akhir 1437 15-01-2016 TAKE:Annabawa Rahama ne ga Al'umma. Bayan yabo ga Allah(swa)da salati ga Annabi(s.a.w.)Mal.ya karanta ayoyi 3 da khutbatul hajah. Bayan haka a cikin Hudubar sa ta farko ya kira Jama'a da suji tsoron Allah su tsayawa gaskiya a duk halin da suka samu kawunan su a ciki.Ya kuma tunatar da jama'ah cewa duk "abinda ake gani da wuya da wahala idan dai har zai kai mutum zuwa ALjannah to ba wuya bace.Haka kuma duk jin dadi da Walwala da zai kai mutum zuwa wuta to ba jin dadi bane. Yana daga cikin tausayawar da Allah kewa bayin sa aikowar manzannin sa zuwa gare su,ba don wanan ba da mutane sun zamo kamar Dabbobi . Malam yaci gaba da ambato muhimmancin aiko da Manzanni zuwa ga mutane,yana daga ciki cewar; Su Manzanni(as)sune tsani tsakanin Ubangiji da Bayin sa,don karbar umurnin sa da gujewa hanin sa.Kuma fiyayye faga cikin su shine Annabi Muhammad (saw)ya karanto Ayoyi da hadisai wadanda suka tabbatar da haka. Ya cigaba da baya ni cewa babu Wanda Allah ya bawa annabta face an samu fajirai da Jahilai da Makaryata da Shaidanu sunyi kokarin ja-in-ja dashi,har ya kawo ayoyi guda 3 a Cikin suratush- Shu'ara Aya ta 221-223. A Huduba ta biyu Mal.yayi magana akan Mu'ujiza da Allah ya bawa Annabawan sa (as)daban daban . A inda yayi magana akan Annabi Musa(as)cewa Allah ya aiko shi a lokacin da sihiri ke tashe ,sai Allah ya hore masa sanda,hannu da dukan teku,domin ya buwayi dukkan masihirta. Annabi Isah(as)Kumar Allah ya aiko shi a lokacin da Likitanci take tashe .Sai Allah ya hore masa warkar da makafi,kutare kai har da tayar da matattu,domin ya buwayi dukkan wani mai magani. Shi kuma manzon Rahama Muhammad (saw)Allah ya aiko shi a lokacin da Fasaha,Balaga dss suke ta she.Sai Allah ya hore masa Alqur'ani domin ya buwayi dukkan wani mai fasaha a Duniya Balarabe ne ko Ba'ajame. Daga karshe yayi addu'a ga Musulunci da Musulmi baki daya Bashir A.Umar Chairman JIBWIS Social Media Rimi 5-Rabi'ul Akhir 1437 15-01-2016. Domin shiga Dandalinmu na Facebook sai ka bi ta wannan Link di Kamar haka: https://mobile.facebook.com/Jibwis-Rimi-488112904601881/
Kungiyar IZALA ta na mika jaje ga Shehu Dahiru Usman Bauchi bisa Gobara da Allah ya kawo a gidansa dake unguwar Makera a cikin Jihar Bauchi. a yammancin Talata da misalin karfe 5:30 na yamma. Rahotanni sunce Gobarar ta cinye gidan kurmus,amma Masallacin gidan bai kone ba. har ila yau majiyar mu ta 'Zuma Times Hausa' ta nakalto cewa ba a samu hasarar rai ba, haka nan ba iya tantance irin yawan hasarar da aka yi ba. Muna addu'ar Allah ya maida alkhairi ya kare gaba, ya kuma kare dukkan musulmai muminai da wannan jarrabawa. Amin. Jibwis Nigeria 02/Rabi Al-Akhar/1437 12/January/2016
KUNGIYAR IZALA TA BUDE ASIBITIN MARAYU A FUNTUA. A jiya Alhamis ne aka samarda wani dan Karamin Asibiti mai dauke da bangarorin duba marayu marasa lafiya a uguwar Ibrahim ward dake garin Funtua. Mal Bishir Usman, shine Shugaban Kwamitin Marayun Unguwar Ibrahim, Ya yi bayanin cewar sun fadada tallafin da ake ba Marayun ne zuwa bangaren lafiya kari akan abinci, sutura, da ilimi da aka dade ana tallafawa Marayun dasu. Shugaban Kwamitin Marayun Funtua LG, Mal Umar Shu'aibu, Ya ce wannan shine karo na farko da aka bada irin wannan tallafin ga Marayu. Ya kuma yi kira ga jama'a dasu kara kokari wajen tallafawa Marayu. Shima Shugaban Kwamitin Marayun na Kasa, Ambassador Abdullahi G. Aminchi, yace tallafawa Marayu aiki ne na kowa-da-kowa. Ya yi kira ga sauran Kwamitocin Marayun dake Karamar Hukumar Funtua da kuma sauran Kananan Hukumomin jihar Katsina da ma na Najeriya gaba daya, suyi koyi da irin wannan aiki. Mal. Sulaiman bin Sulaiman (Limamin Masallacin babbar rumfa) da kuma Mal. Muhammad Sulaiman duk sun yi nasihohi akan mahimmanci da kuma Ladar da ke cikin tallafawa Marayu. Bangarorin da aka samar awurin sun hada da wurin amsar kati, wurin gwajin jini, duba lafiyar hakora, bada shawarwari dama bayarda maganin kyauta ga marayun. Muhammad Lawal Magaji, Jibwis Social Media Funtua. 27/03/1437H 08/01/2016M
Assalamu Alaikum Warahmatullah A madadi Qungiyar JIBWIS SOCIAL MEDIA ta Rimi muna farin cikin sanar da Exco 14 da garemu cewa muna da Bukatuwar Sallar Jumaah na Mabanbantan Masallaci domin yadawa a Kafar Sadarwa ta JIBWIS NIGERIA dakuma ta Jiha watau JIBWIS KATSINA, a karamar Hukumar Rimi munada bukatar Khudubar Masallatai kamar haka: 1. JIBWIS JUMAAT MOSQUE K/YAMMA (M. BASHIR ABUBAKAR UMAR/ALIYU YUSUF) 2. JIBWIS ABUKUR B/TASHA (ALIYU ISHAQ ABUKUR & FARHAN TUKUR ABUKUR) 3. JIBWIS TSAGERO MOSQUE B/KASUWA (M.BATURE DAUDA & YUSUF KHALID) 4. JIBWIS KADANDANI (ANY ONE) 5. JIBWIS MASABO/KURABAU (ANY ONE) 6. JIBWIS MAJEN GOBIR (ANY ONE) 7. JIBWIS MAKURDA (ANY ONE) 8. JIBWIS FARDAMI (ANYONE) 9. JIBWIS SABON GARI (ANYONE) 10. JIBWIS IYATAWA (ZAHARADDEN BELLO & OTHER ONE). Dukan wanda ya dauko zai turo ta a Private Na RIMI JIBWIS SOCIAL MEDIA don tacewa da Takaicewa. Ga Duk wanda yake da bukatar ya rika dauko mana wadannan Khudubobi a Rubuce zai iya yi mana Magana Direct ta JIBWIS RIMI SOCIAL MEDIA ta Link Kamar haka www.facebook.com/Jibwis-Rimi kokuma ta Email kamar haka: Jibwisrimi@gmail.com Sannan zaku iya aikowa da Hudubar Jumaar a takaice domin Isar da sakon Shima a takaice. Mungode Jameel Ahmad Rimi >>>>Secretary<<<<< Jibwis Rimi Social Media For Chairman Malam Bashir Abubakar Umar 20 Rabiul Awwal 1437AH 01/01/2016