Top Local Places

Jibwis Kaltungo Social Media

www.facebook.com/jibwiskaltungo, Kaltungo, Nigeria
Community organization

Description

ad

This page is creat for the eradicating of bid'ah and establishing sunnah  @[286719421452969:0]

RECENT FACEBOOK POSTS

facebook.com

facebook.com

facebook.com

Duk matsalar da musulmai suke ciki yau. Ba laifin kowa sai laifin kawunansu. Allah baya zaluntar bawansa komai, sai dai bawan ya zalunce kansa.. Allah(subhanahuwata'ala) yace: ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻳﻈﻠﻢ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺷﻴﺌﺎ ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻳﻈﻠﻤﻮﻥ. Lalle ne Allah ba Ya zãluntar mutãne da kõme, amma mutãnen ne ke zãluntar kansu. Saboda haka in Mutane suna zama cikin jin dadi da nishadi, sai suka saba masa suka ki bin dokokinsa, toh hakika sai Allah ya jarrabesu..... ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺎ ﻳﻐﻴﺮ ﻣﺎ ﺑﻘﻮﻡ ﺣﺘﻰ ﻳﻐﻴﺮﻭﺍ ﻣﺎ ﺑﺄﻧﻔﺴﻬﻢ Lalle ne Allah bã Ya canja abin da yake ga mutãne sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Saboda haka 'yan'uwa hanya dayace tak zata kaimu ga fita daga cikin wannan matsasi da wahala. Hanyar kuwa itace 'Bin Tafarkin magabatanmu salihai na farko, ta yadda suka sami izza a lokacin da Duniyar kafurci take Kewaye dasu, toh muma haka zamubi mu sami izza in mukabi tafarkin yadda suka bi. 'Muyi riko da dokar Allah, sannan mu kaurace wa Zunubai manya da kanana. Sannan kuma muso juna. Allah yasa mudace ya yaye mana duk wata matsalolinmu...

facebook.com

facebook.com

facebook.com

facebook.com

*BABU ASKI DA YANKE FARSHE GA MAI NIYYAR YIN LAYYA IDAN ZUL HIJJA YA KAMA:* ✍🏼 Rubutawa: *Sheik Dr Ibrahim Jalo Jalingo (Hafizahullah)* 1. Da zarar an ce watan Zul Hijjah ya kama to dukkan mai niyyar yin layya kada ya aske wani gashi a jikinsa, haka nan kada ya yanke farshensa sai bayan ya yanka layyar tasa. Saboda Imam Muslim ya ruwaito Hadithi na 1977, da Nasaa'iy Hadithi na 4364, da Ibnu Majah Hadithi na 3149, da Ahmad Hadithi na 26,517, da Tabraaniy Hadithi na 19,063, da Daaramiy Hadithi na 1,948, da Ishaq Bin Raahuyyah Hadithi na 1815 daga Nana Ummu Salamah Allah Ya kara mata yarda ta ce Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:- ((اذا رايتم هلال ذي الحجة واراد احدكم ان يضحي فليمسك عن شعره واظفاره)). وفِي رواية: فلا يأخذن شعرا ولا يقلمن ظفرا)). وفِي رواية: ((فلا يمس من شعره وبشره شيئا)). Ma'ana: ((Idan kun ga jinjirin watau Zul hijjah sannan dayanku ya yi nufin ya yi layya to ya kame ga barin gashinsa da farshensa)). A wata riwayar: ((Kada ya dauke wani abu na gashi, kada ya yanke wani abu na farshe)). A wata riwayar: ((Kada ya taba wani abu na gashinsa da fatar jikinsa)). 2. KO ZA A HANA WA MACE MAI SON YIN LAYYA TSEFE GASHI DA KITSO? To amma mace mai niyyar yin layya ko da yake ita ma ba za ta yanke farshenta ba, ba za ta kuma aske wani gashi daga jikinta ba, to amma abin da zahirin nassi ke nunawa shi ne: tana da damar ta tsefe kanta ta yi kitso; saboda Imamul Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 316, da Imamu Muslim Hadithi na 1211 daga Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:- ((أهللت مع رسول الله صلى الله عليه وسلم في حجة الوداع فكنت ممن تمتع ولَم يسق الهدي فزعمت انها حاضت ولَم تطهر حتى دخلت ليلة عرفة فقالت: يا رسول الله هذه ليلة عرفة وإنما كنت تمتعت بعمرة، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: انقضي رأسك وامتشطي وأهلي بالحج ودعي العمرة)). Ma'ana: ((Na shiga aikin hajji tare da manzon Allah mai tsira da amincin Allah a shekarar hajjin ban kwana, na kuma kasance daga cikin wadanda suka yi tamattu'i ba su koro dabbar hadaya ba. Ta ce sai haila ta zo mata, ba ta kuma yi tsarki ba har dai daren Arafah ya shigo, ta ce sai na ce: Ya manzon Allah wannan dai daren Arafah ne, ni kuma da ma ina cikin umrar tamattu'i ne? Sai manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: "Ki warware kitson kanki, ki tsefe shi, ki shiga yin talbiyyar hajji, ki kyale Umrar)). Mahallush shaahid a nan shi ne: Annabi mai tsira da amincin Allah ya ba wa Nana A'isha izinin ta warware kitsonta ta kuma tsefe gashin kanta, duk kuwa da cewa tana cikin Ihraami ne shi kuma mai Ihraami sawaa'un mace ce ko kuwa namiji ne ba yi da damar aske gashinsa ko yanke farshensa. To amma kuma ga shi an ce A'isha tana iya kwance kitso tana kuma iya tsefe gashi, ke nan akwai banbancin hukunci tsakanin: aske gashi da yanke farshe, da kuma kwance kitso da tsefe gashi. 3. Ke nan wannan yana gwada mana cewa: Mace mai niyyar yin layya idan watan Zul jijjah ya kama kada ta yanke farshenta, kada kuma ta aske gashin wani bangare na jikinta, to amma tana da damar ta warware kitsonta ta yi wani sabon kitso. Allah Ya taimake mu Ya ba mu dabbobin da za mu yanka a matsayin layya, Ya kuma karba mana ibadodinmu. Ameen.

facebook.com

facebook.com

A KOWACE SAFIYA DAN ADAM YANA HADUWA DA BALA'I GUDA UKKU . Na farko 1 . Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka. Idan kudinsa ya ragu xai tuhuma bayan kudi yana dawowa amma shekaru basa dawowa. . Na biyu 2 . kullum yana cin arxikin Allah in halal yaci xa'a tambaye shi in haram ne xa'ayi masa axaba akai bai san karshen hisabin mai xai kasanceba. . Na uku 3 . kullun yana kusantar lahira yana nisantar duniya amma duk da haka baya damuwa da lahira kamar yadda yadamu da duniya Bai san makomarsa ba shin aljannace ko wutace. . Gaskiya . (Babu abunda xai amfaneka sai sallarka). . wanda yabar karatun Alqur,ani tsawon kwana uku ba tare da uxuriba sunansa maqauraci (wanda ya qauracewa Alqur,ani kenan). Nasiha ce,

facebook.com

Allah ya Maimaita mana ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺣَﻮَﺍﻟَﻴْﻨَﺎ ﻭَﻟَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻨَﺎ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﺂﻛَﺎﻡِ ﻭَﺍﻟﻈِّﺮَﺍﺏِ ﻭَﺑُﻄُﻮﻥِ ﺍﻟْﺄَﻭْﺩِﻳَﺔِ ﻭَﻣَﻨَﺎﺑِﺖِ ﺍﻟﺸَّﺠَﺮِ

facebook.com

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Abubakar Sa’ad III, Ya bada Sanarwan ganin jinjirin watan Shawwal a Naijeriya, gobe Lahadi 25/06/2017. Zai zama 01 ga watan Shawwal kuma ranar Idin Karamar sallah insha Allah

facebook.com

ABUBUWAN DA SUKE WAJIBI AKAN MAI AZUMI. Kashi Na farko. Daga Musa H Musa Kayi sani yakai dan'uwa musulmi lallai Allah ta'ala ya farlanta azumi akanmune saboda mubautamasa dashi, saboda azuminka yakasance karbebbe, mai fa'ida, ka'aikata abun da zaizo. 1. KAKIYAYE SALLAH: dayawa dagacikin masu azumi suna wasa da sallah, kuma itace ginshikin addini barinta kuma yanadaga cikin kafurci. 2. Kakasance mai kyakkyawan dabi'a kuma kanisanci aikin kafurci da zagin mai'addini da mummunan mu'amala tareda mutane kana mai kafa hujja da Azuminka, shi Azumi yana tarbiyantadda rai, karka munana dabi'unka, shikuma kafurci yana fitadda mutum daga musulunci. 3. Karkayi yasashiyar magana koda a rahane. don zai batama azuminka, kasaurari maganar manzo s.a.w inda yakecewa. ((Idan ranan Azumin dayanku yakasance kada yayi Alfasha cikin magana. Kuma kada yayi fada idan wani ya zageshi ko yanemi fada dashi yace lallai ni ina Azumi, ni ina azumi)) 4 ka tsayu da azuminka wajen barin shantaba wanda yake janyomaka zagwanyewa da kuraje, kuma kakasance mai tsayayyen iko akai, karkasha dadaddare kamar yadda kabarshi darana, sai kaga lafiyarka tacika hakama dukiyarka . 5 Karkayi Almubazzaranci da abinci yayin buda baki don karka bata fa'idar azuminka kuma karka cutar da lafiyarka. 6.kada kaje sinima (gidan kallo) haka kuma kada kakalli vidio fina-finai saboda kada kakalli abun da zai bata dabi'unka kuma ya tafiyadda ladan Azuminka. ZAM UCIGABA DAYARDAR ALLAH. MUNA ROKON ALLAH YADATAR DAMU. Musa H Musa 4/Ramadan/1438

facebook.com

Quiz

NEAR Jibwis Kaltungo Social Media